Sanarwar ta ce gwamnatin za ta gina gadar ne da kudin da za ta aro daga Babban Bankin Najeriya, kuma kafin gwamnatin ta kammala wa'adinta za ta biya kudin. "Amma kuma a baya akwai alamun gwamnatin tarayya na shirin aiwatar da aikin gina gadar tun da dama titin Kano zuwa Maiduguri da gadar za ta ratsa na gwamnatin tarayya ne. "Amma a yanzun ma bai ɓaci ba, gwamnatin jiha na iya farawa sai dai zai yi kyau su yi yarjejeniya da gwamnatin tarayya ta biya ta kuɗaɗen da ta kashe bayan kammala aikin. Tun kafin gwamnatin ta amince da gina wannan gada ta shataletalen Hotoro, wasu mutanen jihar na da ra'ayin cewa kamata ya yi gwamnatin ta mayar da hankali kan samar da ruwa da inganta harkar lafiya. Nura Mustapha Wudil ma ya ce: "Raya zukatan ɗan Adam shi ne abin da ya kamata gwamnati ta mayar da hankali a kai.
Source: GhanaWeb March 31, 2021 16:18 UTC