'Yan Bindiga Sun Sace Wasu Mutum 3 Da Kona Motar Jami'an Tsaro a Jihar Neja - News Summed Up

'Yan Bindiga Sun Sace Wasu Mutum 3 Da Kona Motar Jami'an Tsaro a Jihar Neja


Jihar Neja - Ƴan bindiga sun sake kai farmaki a Garin Gabas kusa da Yakila a ƙaramar hukumar Rafi ta jihar Neja inda suka sace mutum uku. Jaridar Leadership ta kawo rahoto cewa ƴan bindigan sun raunata jami'an tsaro mutum biyu sannan suka ƙona motocinsu guda biyu. Gwamnan jihar Neja ya yi martani kan harinDa yake martani kan harin, gwamna Mohammed Umaru Bago, ya nuna alhininsa ga masarautar Kagara kan harin inda ya yi alƙawarin kawo ƙarshen matsalar tsaro a jihar, rahoton Thisday ya tabbatar. Gwamna Bago a cikin wata sanarwa da kakakinsa, Bologi Ibrahim ya fitar, ya bayyana harin a matsayin abun takaici sannan ya jajantawa iyalan waɗanda harin ya ritsa da su. Gwamnan ya roƙi al'ummar jihar da su ƙara yi wa gwamnatinsa uzuri domin baya wasa da duk wani abu dangane da kare lafiya da dukiyar al'ummar jihar.


Source: The Guardian July 25, 2023 15:03 UTC



Loading...
Loading...
  

Loading...

                           
/* -------------------------- overlay advertisemnt -------------------------- */