Ya shaida wa BBC cewa: "Lokacin ibadar aikin Hajji, da watan Ramadan, da lokacin Ashura da Tasu'a suna da alaka da watannin Musulunci. Maram Kairé, shi ne shugaban kungiyar masana taurari a Senegal, ya kwashe shekara da shekaru yana kokarin ganin an yi amfani da ilimin kimiyya wajen ganin wata. Amma duk da haka wasu musulmai na kasar suka yanke shawarar fara azumi ta dogaro da ganin watan da wasu kasashen duniya suka yi. Ma'aikatar harkokin addinin Musulunci da Hubusi, ta sanar da ganin wata da fara Azumin Ramadan a ranar Laraba 14 ga watan Afirilu 2021. Hakan ya faru saboda rashin ganin watan a ranar Talata kamar yadda kwamitin ganin watan ya bayyana.


Source:   GhanaWeb
April 15, 2021 03:22 UTC